متن احکام
(M: 970): A na kallon azumi a matsayin ibadar da Allah ya sanya wa mutane, ta yadda yin niyyar sa biyaiya ce da neman dacewar Allah (s.a.w), darsa niyyar yin sa kadai ta isa a matsayin niyya ko da kuwa bisa dogaro ne, ba dole sai an furta niyyar a baki ba duk da cewa yi a bakin ya fi, haka nan ma cikin niyyar ba dole sai ya hada da nufin rashin karya azumi cikin ta (niyyar), azumi kuma ba ya cutuwa da rashin niyyar matukar an tashi da shi ko chanja ja azumin da ya niyyata zuwa wani azumin, kuma ba dole sai ya kudurci tsawon lokacin azumin sa a niyya ba ko wani dan lokaci cikin lokacin azumin, haka nan ma yin baccin gaba dayan lokacin azumi ba ya cutar da azumi balle yin baccin wani dan lokaci yayi azumi, amman kuma idan mutum ya yi farfadiya ko maye (buguwa) cikin baccin (sa lokacin) azumi sai ya farka da rana to ya cika azumin sa (azumin ya yi bia fatawa) idan bai cika azumin ba ramuwa ta kama shi, amma idan buguwa ya yi cikin baccin bayan niyya kuma ya farka kafin lokacin shan ruwa to yankan shakku shi ne ya cika azumin kuma ya rama shi.
*(M: 971): Ba dole sai mutum ya kudurce niyyar wajabci, biyayya, ramuwa ko wanin sa da nufin lallai sai ya ayyana shi kamar ramuwa ko kaffara – kamar yadda bayani ke zuwa – abin da a ke bukatar a kudurce, idan aka hade niyyar sa waje daya (idan azumin sama da daya ne) ya isar.
*(M: 972): A na bukatar kudurce niyyar azumin ramuwa, jin niyyar rama azumin da ya gabata ya wadatar, a na lura da cewar idan za a rama azumi a fara azumin har a gama, ko da bai niyyace shi ba ya isar masa fara azumin, idan kuma niyyar daya-daya ya yi cikin da yawa daga azumin ramuwa ko wanin sa niyya daya ta isar masa.
*(M: 973): A na lura cikin azumi da – abubuwa kamar yadda ya gabata – niyyar sa ta yi daidai idan ya hada ta baki daya matukar ya kudurce ta tsakanin sauran ibadu, haka nan abin ya ke ga wanda ya kudurce rashin ci da sha da sauran dokokin shari'a (wajan karya azumi), ba dole sai ya baiyana gudun abubuwan da kan iya bata masa azumi, da bai bayyana wasu daga abubuwan da kan iya bata azumi ba – kamar jima'i – ko nufin rashin karya azumi ba zai cutar da azuminsa ba.
*(M: 974): Babu damar yin wani azumin da ba na ramadana ba cikin watan ramadana, ko da mai azumin ba azumi a kan sa kamar matafiyi, idan ya yi niyyar yin wani azumin ba ramadanan ba azumin sa bai yi ba, haka nan ma idan bai warware niyyar sa (ta yin wani azumin) ba domin kusanci ba – da kuma bai san a cikin ramadan ya ke ba ko ya manta to a nan azumin sa ya yi (a matsayin na ramadan) sai ya bar shi (azumin) a matsayin na ramadan ba wanda ya yi niyya ba da farko.
*(M: 975): Azumi ya inganta yayin da aka tashi da shi, ba wai dole sai an tantance niyyar sa ba (matukar an yi niyyar tashi da shi), sai dai amman domin yanke shakka an so kudurce niyyar sa ko da lokaci daya ne da nufin zai tashi da azumin wajibi gobe, haka nan ma abin ya ke game da azumin da ya ke na neman lada a kan gina niyya kan neman kusancin Allah (s.a.w) amman a lokacin da ya halatta ya yi azumin (neman ladan) kuma mai azumin ya na da damar ya yi azumin ba tare da matsalar hukuncin rashin azumi a kan sa ba kamar matafiyi ko wanda a ke bin sa bashin azumin ramadan, haka ma abin ya ke a kan azumin bakance da bangarorin bakancen, sai dai in an takaita niyyar kamar azumi don godiya ga Allah ko tsawa, misalin sa ramuwa da kaffara da makamantan wannan idan bai tsayar da rana ko lokacin da zai yi azumin ba, na'am amman idan ya yi nufin cikin niyyar sa da zai yi guda daya wannan ya isar masa.
*(M: 976): Lokacin wajabcin niyyar da aka ayyana na yiyuwa ne ko da a daidai ketowar al'fijir na gaskiya ne amman bisa yankan shakku (ihtiyadi), a na nufin mai azumi ya niyyace kame baki tare da niyyar azumi ko da da ka ne ba kuma a na nufin a kwai wani tsayayyen lokacin da ake buktar niyya cikin sa ba, amman azumin wajibi lokacin niyyar sa na kaiwa har zuwa zawali (tsakkiyar rana) sai dai wannan lokacin kurarre ne, amman mai azumi na da daman jinkirta niyyar sa bisa zabi, da mutum zai wayi gari na nufin yin wani abun da kan iya karya azumi sai ta bayyana gare shi cewa azumi ya kama kafin zawali kuma ya niyyaci yin azumin wajibi azumin sa ya yi, amman idan bayan zawali (tsakkiyar rana) ya fahim ci haka bisa yakkan shakku (ihtiyadi) an so ya sake azumi, amman idan azumin neman lada ne lokacin sa niyyar sa kan zama har zuwa gwargwadon lokacin da ke tsakanin faduwar rana da gama niyyar.
*(M: 977): Niyya daya ta isar wa azumin ramadana dukkan sa kafin shigowar watan, ba bukatar yin niyyar daukan azumi cikin kowane dare ko yayin fitowar alfijir, duk da cewa ana bukatar hakan ko da ka ne – kamar yadda mu ka yi bayani a baya – haka nan ma ko da ba a azumin ramadana ba ne, kamar azumin ramuwa da makamantan sa.
*(M: 978): Idan mutum ya manta yin niyyar azumin ramadan, saboda manta huknci, maudu'i ko rashin sanin wani hukunci sa da maudu'in ba kuma bai yi wani abu da ke karya azumi ba sai ya tuna (hukuncin) ko ya san (abin da ya jahilta da farko) da rana yana da damar sabunta niyyar sa kafin tsakkiyar rana (zawali), amman fa akwai matsala fa idan hakan ta faru an so domin yakke shakka ga azumin sa ya sabunta niyya ya cika azumi kuma ya rama azumin bayan ramadan.
*(M: 979): Idan ya yi azumi ranar da ya ke kokwanton cewa shin sha'abn ne ko ramadan don neman lada amman sai ta bayyanar masa cewa ranar cikin ramadana ya ke azumin sa ya yi a matsayin na ramadana, da a ce ta nayyana gare shi cewa cikin ramadana ya ke kafin tsakkiyar rana ko bayan sa kawai sabunta niyya zai yi, amman idan da niyyar ramadana ya dauki azumin to bai yi ba, idan kuma ya azumta ne don wani abu na daban ne ya kan iya juyar da azumin sa zuwa wanin – amma bisa wajabci ko neman lada – azumin ya inganta, idan ranar ta zamo cikin sha'aban ne azumin sa ya zama na neman lada haka ma ko da ranar cikin ramadana ce (azumin sa ya yi), wanda bai yi niyyar tashi da azumi ba sai da gari ya waye ya fahimci ramadana ya tsaya hukuncin sa na cikin tambayar da ta gabata.
*(M: 980): Ya wajaba a dauwwama niyya har zuwa karshen rana, in ya yi nufin yanke azumi ko ya yi kokwanto azumin sa ya baci in kuwa ya dawo wa niyyar yin azumin a nan ana bukatar niyyar sa bisa yankan shakku, haka nan ma in ya yi nufin yanke azumi kamar abin da ya zo ko kaikawo cikin sa ko kuma niyyar katse azumin ya yi tare da sanin karya azumin, yin kawo bisa shakku kan ingancin azumi ba ya cutar da shi (azumin), wannan haka ya ke cikin wajibin bayyananne, amman cikin wajibin da ba bayyananne ba ba ya ba ya sauke wani abu daga gareshi idan ya dawo kan niyyar sa kafin zawali.
*(M: 981): Ba ya inganta ciratuwa daga wani azumi zuwa wani koda ya dauwwama cikin lokacin azumi na biyun (da ake nufin komawa gare shi), na'am sai dai in bai aiyyana ainihin (kalar) azumin farkon ba bai kuma kaiyyade rashin niyyar na biyun ba – idan kuma bai yi nufin ciratuwar na farkon zuwa na biyun ba, to na farkon ya yi na biyun kuma ya baci, misali: da zai yi nufin yin azumin ramuwa sai ya yi nufin ya canja shi zuwa na neman lada (nafila) to na biyun (nafilar) ya inganta na farkon (na ramuwar) ya baci, da kuma zai nufin yin na nafila ya canja shi zuwa na ramuwa a nan sai ya zama na nafilar (farkon) ne ya inganta banda na ramuwar (farkon).