متن احکام
Azumi na karyewa saboda abubuwa masu zuwa:
Na farko, Na biyu: ci da sha, komai kankantar abin da aka ci ko aka sha, kadan ko da yawa, kai ko ma a ce bakin abubuwa ne.
*(M: 982): Bai wajaba a yi sakace bayan ci ga wanda ke son yin azumi ba, koda idan bai yi ba ragowa kan iya makalewa tsakankanin hakoran sa wanda zai iya kai wani abu makogaron sa, haka nan ma azumi baya baci in hakan ta faru bisa mantuwa, amma fa idan ya san hakan zai faru wajibi ne ya sakace shi (abin da ke hakorin na sa).
*(M: 983): Domin yanke shakka a na son kada mutum ya hadiyi abin da ya fito daga kirjin sa zuwa baki ko abin da ya taho daga kansa kamar majina matukar ta shiga farfajiyar bakin sa, amman idan (abin da ya fito daga kirji ko kain) ba su shiga farfajiyar bakin ba ba matsala.
*(M: 984): Babu laifin game da miyan da ke taruwa a baki koda ya na da yawa ne ko da ya na sane ya tara yawun sabida tuna (ko kallon) wani abu mai tsami.
*(M: 985): Ba laifi shigar wani abu cikin ciki matukar ba ta makogaro ya bi ba matukar ba za a kira shi ci ko sha ba – banda wanda aka shigar da ruwa jikin sa kamar – da za a sa magani a ciwon sa, kunnen sa ko cikin 0000 ya shiga cikin ciki a nan ba azumin sa garau, haka nan idan a ka soke shi da mashi ko wuka ya/ta shiga cikin sa da makamantan su, na'am idan da wani abu zai shiga cikin sa irin shgar abinci amman ba ta makogaro ba wanda za a iya kiran sa ci ko sha a cikin sa nan sai mu ce ramuwa ta kama shi domin kuwa azumin sa ya karye kamar wanda ya je shakar ruwa sai ruwan ya shiga cikin sa ta hanci, amman shigar magani kamar shigar da abinci ta hanyar allura ko tube da a ke sawa ta hanci zuwa cikin ciki ko ta cikin jijiya wannan babu laifi, haka nan diga magani cikin ido ko kunne koda kalar su ko dandanon su sun baiyyana cikin makogaro.
Na uku: Jima'i ta gaba ko ta baya, wanda ya yi da wanda aka yi wa, da matacce ne ko rayayye.
Da mutum zai nufin jima'i sai ya yiu kokwanton shiga ko nitsewar hashafa (kan kaciya) a na sanya shi cikin masu nufin karya azumi kuma hukuncin sa ya gabata, sai dai kaffara ba ta kama shi ba. Haka ma azumin sa na nan idan da nufin yin amfani da cinya hakan ta faru – misali – sai ya shiga dayan kofofi biyu ba tare da nufin hakan ba.
*(M: 986): Ba bambanci kan bacin azumi da yin jima'i ya/ta kawo ko a'a.
*(M: 987): Idan mutum ya yi jima'i bisa mantuwa kwatsam sai ya tuna wajibi ne ya yi gaggawar cire al'aurar sa idan ya yi jikiri azumin sa ya baci.
*Na hudu: Yin karya ga Allah ko Manzon sa (SAW) ko a kan wasiyyan manzon sa (AS) amman (na wasiyyan) bisa yankan shakku mafi inganci, kai a yankan shakku mafi cancanta har ma kan sauran Annabawa da wasiyyan su (AS), ba tare da bambancin karyar da ya yi kan lamarin duniya ne ko na addini, idan ya yi nufin yin karya gare su (wadanda muka ambata) sai ta bayyana cewar ashe gaskiya ne azumin sa na nan, ko ya yi nufin karya sai ta bayyana ya fadi gaskiya a nan hukuncin sa na wanda ya yi nufin karya azumi ne, kamar yadda hukuncin sa ya gabata.
*(M: 988): Idan ya yi karyar da bai jinginawa kowa ba, ko ya yi ta ga wanda bai fahimci karyar ba amman wanda ba shi aka gayawa karyar ba ya fahimta ko ya bijiro ta ga wani ya ji – kamar ya rubuta da wani abu (ba tare da ya furta ba) – ta a nan yankan shakkun da ya gabata ya kama shi (na hukuncin wanda ya yi niyyar karya azumi).
*Na biyar: Nutsa baki dayan kan sa baki daya a wajan mashahuran malaman fikihu (RA), amman a wajan mu shine cewar wannan ba ya karya azumi sai dai amman makaruhi ne mai tsanani, ba kuma bambanci wajan dulmiya kan na sa a hankali ko baki daya, ba laifi a tsoma rabin kai sannan a tsoma rabin daga baya koda nutsewar ce, haka nan hukuncin ya ke wajan yin kundumbala baki daya kamar yadda masu nutso ke yi.
*(M: 989): Babu jirkitaccen ruwa (sai mai tsakakewa) cikin hukuncin da ya gabata.
*(M: 990): Yankan shakku da aka fi so ga mai azumi (kowanne iri) kada ya dulmiya kan sa cikin ruwa.
*Na shida: Gangancin shiga cikin kakkaurar kura ko hayaki cikin makogaro amman don yanke shakka (inganta azumi), amman ba laifi ga marasa kaurin su, ko ga wanda ya kasa guje musu kamar irin kura mai kauri wadda iska ke tasa.
*Na bakwai: Gangancin wanzuwa cikin janaba har zuwa ketowar al'fijir, amman wannan hukuncin ya kebanta ne kan azumin radana da ramuwar sa, ba haka abin ya ke ba dangane da azumin wajibi ko na nafila.
*(M: 991): Wanda ya kasa samun tsarki biyu ba shi da hukunci irin na mai ganganci don haka sai ya ci gaba da azumin cikin janabar (kafin samun damar tsarki).
*(M: 992): Yin asubanci cikin janaba ba ya baga azumi matukar ba bisa ganganci ko sakaci hakan ta faru ba, abin haka ya ke kan azumin ramadana da sauran su, har da ramuwar ramadana – amman fa idan lokaci bai kure masa ba – idan bai samu ba barin sa ya fi domin yanke shakka.
*(M: 993): azumi ba ya baci – na wajabci ne ko na nafila – ayyananne ko ba ayyananne ba – don yin mafarki cikin dare, kamar yadda azumi ba ya baci wanzuwa cikin hadasin taba matacce bisa ganganci har fitowar al'fijir.
*(M: 994): Idan mutum ya samu janaba da gangan cikin dare kuma ya san ba zai iya wanka ko yin taimama ba hukuncin wanda ya yi gangnacin zama da janaba ya kama shi, na'am amman idan ya na da damar yin taimama wajibi ya yi taimama don daukar azumi, duk da haka don ya yanke shakka ya rama, idan da zai ki yin taimamar kuma a wannan halin ramuwa da kaffara sun kama shi.
*(M: 995): Idan mutum ya manta yin wankan janaba da daddare har ya kwana ko kwana nawa ne cikin ramdana azmin sa ya baci kuma ramuwa ta kama shi, amman banda azumin da ba na ramadana koda na wajibi ne, amman da hakan za ta faru kan wanin na ramadana (ana son) ya rama domin bukatar yanke shakka, kamar yadda ba a riskar da wankan jinin haila ko na haihuwa idan mace ta manta wankan janaba shi ma din a na son hade shi domin yanke shakka.
*(M: 996): Da mai janaba zai kasa samun damar yin wanka sabida rashin lafiya da makamantan su wajibi ya yi taimama kafin ketowar alfijir, idan bai yi (taimamar) ba azumin sa batacce ne, haka nan ma idan ya yi taimamar ba dole ne sai ya zauna har ketowar al'fijir ba, bisa yankan shakku kuma an so yin hakan.
*(M: 997): Idan mutum na tsammanin isar lokaci ya janabantu sai ta bayyanar masa ashe lokacin ya yi masa karanci ko da ma yin taimama ne ba (laifin) komai a kan sa duk da cewa ramuwa ta fi masa domin yanke shakku sabida rashin kiyayewa.
*(M: 998): Hukuncin mai haila ko jinin haihuwa daya ne da na mai janaba idan ya/ta yi gangancin zama cikin rashin tsarki domin azumi na baci amman na ramadan kawai banda wanin sa ramuwa na kan wanda ya yi haka don yanke shakka, idan kuma ta/an samu damar yin wankan a lokacin da ba zai isa a yi wanka ko taimama ba ko rashin sanin tsarkin sa/ta har zuwa fitowar rana azumin ya inganta.
*(M: 999): Hukuncin macen da ke jinin istihala (cuta) dan kadan daya ne da na mai tsarki haka nan ma abun ya ke kan matsaikaci ko jini mai yawa, ba a bukatar sai ta yi wanka azumin ta ya yi, an so don yake shakka ta yi wankan rana ko dann salla ne.
*(M: 1000): Idan mutum ya yi janaba da daddare ya kuma kwanta har hari ya waye, idan ya kwanta da niyyyar ba zai wanka ba hukuncin wanda ya zauna cikin janaba bisa ganganci ya hau kan sa, haka nan idan ya yi baccin ya na kaikawo kan yiyuwar wankan amman hakan bisa yankan shakka (ihtiyadi) ya shiga hukuncin mai ganganci, idan kuma ya yi baccin da nufin tashi wanka kuma ya tashi kafinkurewar lokaci ba matsala matukar zai iya kiyaye tashi, idan kuma bai niyyar tashi ba kuma ya ki tashin ihtiyadi shi ne ya rama azumin, idan ya koma bacci na biyu – abin nufi ya yi bacci ya farka bayan sanin janabar sa sannan ya koma bacci na biyu har gari ya waye – ramuwa ta kama shi ba tare da , haka ma ko da a bacci na uku ne an so ya yi kaffara bisa yankan shakku (ihtiyadi), haka ma ko da hakan ta faru ne a baccin farko da na biyu matukar bai kwanta da niyyar wanka ba. Idan ya yi bacci cikin gajiya ya rafkana ga yin wanka – don azumin goben ba – dole ya rama azumin, amman yankan shakkun da ya fi ya yi kaffara idan a bacci na uku ne.
*(M: 1001): Ba laifi ya yi baccin farko da na biyu matukar ya na da tabbacin zai farka don yin wanka kafin al'fijir, bisa yanke shakka an so kada ya ki yin wankan matukar bai da cikakken amincin zai farka, idan ya yi bacci bai farka ba har lokaci ya kure ramuwa ta kama shi ko da a baccin farko ne musamman ma a ce a bacci na uku ne.
*(M: 1002): da mutum zai yi mafarkida rana cikin ramadana kuma ba shi da damar gaggauta wanka ba, zai iya koro abin da ya makale da fitsari idan akwai ragowa cikin al'aurar sa, amman da zai samu damar wanka kadin koro ragowar da fitsari an so ya jinkirta wankan sa zuwa bayan magriba matukar zai iya hakan.
*(M: 1003): A na lissafa farkawar farko cikin baccin da aka yi mafarki da baccin farko, idan ya farka bayan mafarkin ya koma baccin to sanda zai kara tashi wannan baccin sunan sa (bacci) na biyu.
*(M: 1004): Hukncin da ke kan wanda ya yi bacci na uku, daya ne da wanda ya yi na hudu ko na biyar da sauran su.
*(M: 1005): Cikin hukuncin da ya gabata kan kaffarar mai janaba banda mi jinin haila ko nifasi (jinin haihuwa), azumin ta ya inganta matukar ba ta jinkirta wanka da gangan ba koda kuwa abin ya kai ta ga bacci na biyu ko na uku, amman idan jinkirin ne ya jawo haka azumin ta ya baci ko da a baccin farko ne.
Na takwas: Fitar da maniyyi ta hanyar da ake da tabbacin zai iya fita koda bai fitan ba, amma ida ta hanyar da ba a tsammanin fitar sa ya fita bisa tsautsayi ko kwatsam ya fito ba tare da aikata komai ba a nan azumi bai baci ba.
Na tara: shigar wani abu da ya ke ruwa cikin jiki ko da bisa rashin lafiya ne, amman ba laifi ga abin da ya ke mai tauri duk da bisa yankan shakku shi ma din ba a so ba, kamar yadda ba laifi game da abin da mace ke shigar da shi jikin ta na ruwa ko mai tauri cikin mahaifar ta.
*(M: 1006): Idan wani abu mai ruwa ya shiga ciki kamar abin da ya shiga ta dubura ba ya karya azumi amman dai an so barin sa don yanke shakka.
*(M: 1007): Shigar abin da a ke kokwanton shin ruwa ne ko sandararre cikin jiki ya halatta amma don yake shakka an so kar a shigar da shi.
Na goma: Yin amai da gangan koda mai larura ne don magance wata matsala da makamantan sa, amman ba laifi bisa mantuwa ko ba da gangan ba.
*(M: 1008): Shakuwa ta halatta ga mai azumi ko da akwai yiyuwar fitowar wani abu daga cikin sa (ta baki), don yakke shakka an so idan da hali kada mutum ya yi matukar ya sa wani abu kan iya fitowa wanda za a iya ganin sa kamar amai, idan ba haka ba bai halatta ba.
*(M: 1009): Da wani abu zai fito daga sabida gyatsa sai ya koma ba tare da niyyar mayar da shi ba azumin sa na nan, amman da zai shigo cikin baki sannan a mayar da shi da gangan azumin sa ya baci sai ya rama a bisa yankan shakku kuma dole sai ya rama azumin kuma ya hada da kaffara.
*(M: 1010): Idan mutum ya hadiyi wani abu bisa mantuwa amman sai ya tuna kafin shigar sa makogaro wajibi ne ya fito da shi kuma azumin sa na nan, amman da a ce bai tuna ba sai da abin ya kai zuwa inda ba damar ya dawo da shi zuwa cikin bakin sa ba dole sai ya fito da shi ko ya amayo shi ba, idan kuma ya na kokwanto cikin abin da ya gabata dole ya fito da shi.
*(M: 1011): Idan mai azumi ya hadiyi abin da zai yi amansa ko ya sa shi da rana azumin sa ya baci idan ya yi aman da rana, ko da bai niyyaci kin aman ba – matukar ya san zai tashi da azumi – a lokacin da ya san bai kamata ya jinkirta niyya ba bisa gangancin da zai hana ya mike da niyyar sa kamar yadda ya zo cikin (M: 976), ba banbanci takanin sa da wanda ya yi niyyar amai da rana ko da bai yi aman ba.
*(M: 1012): Sanya zobe ba ya karya azumi, ko dafawa yara abinci, ko dandanon da mace ke yi wa abinci da makamantan su matukar ba za su kai ga makogaro ba, ko yin amai tare da niyya ba, manta ya na azumi – da a ce ya na sane ya yi aman azumin sa ya baci ko kadan nen – haka nan ba laifi da dandana ko lasar wani abu ko da an ji dandanon sa a cikin bakin sa – matukar bai wuce ciki ba – ko dayan m'aurata ya tsotsi harshen daya, ihtiyadin da aka fi so a nan kada ya zama akwai danshi a harshen wanda aka tsotsa, sadai an so yin aiki da ihtiyadi wajan.
*(M: 1013): Karahiya ne ga mai azumi ya yi shafi mace, sumbata, ko ya yi wasa da ita kamar yadda magabatan malamai (RA) su ka fada ko da ya na da tabbacin ba zai kawo ba, idan ya yi nufin ya kawo ya na da hukuncin wanda ya yi niyyar karya azumi, karahiya ne ya yi amfani ko alaka da abin da kanshin sa ko dandanin sa zai iya kai cikin makogaro ba kamar Turaren wuta da turare, haka nan shiga lambu don gudun gajiya, fitar da jinin da kan iya sa raunin jiki, shakar da ta shiga makogaro bisa kuskure, shinshina fure mai tsananin kanshi, jika kayan da ke jiki da ruwa, zaman mace cikin ruwa, dogara da wani abu mai tauri da zai amfanar don saukaka azumi, cire hakori ko wani abu da kan iya sa cikin baki jini, asuwaki da danyen itace, wasa da yin kuskurar baki, raira waka sai dai cikin wuraren Ayimmatu Ahlulbait (AS) da yabon su. Ya zo cikin labari cewa: (idan ku na azumi ku kiyaye harsunan ku daga karya, ku kame gannen ku kada ku yi jayayya da hassada da barna da dagawa da karya da yi wa juna mummunan kallo da ku saba da fushi da zagi juna da kunyata juna da jefi juna da munanan kalmomi da jayayya da gayawa juna munanan kalamai da zaluntar juna da wauta da soki juna haka nan ma kada ku gafala daga ambaton Allah (s.a.w)) hadisin na da tsayi.
*KARIN BAYANI
*Abubuwan da mu ka ambata a baya masu warware azumi na warware azumi ne kawa idan a ka aikata bisa ganganci da zabi, amman duk wanda ya afku kan mantuwa ba da niyya ba baya bata azumi, ba tare da banbaci tsakanin azumin wajibi, nafila neman lada ko na dama, da mutum zai fadi fadin Allah (s.a.w) bisa gaskiyar sa sai ta bayyana karya ne a hakika ko ya manta ya na azumi ya yi abin da ke karya azumi ko wani abu ya shga cikin saba da son ransa ba azumin sa bai baci ba, a nan babu bambancin hukuncin tsakanin malami da jahili, na'am ba hukunci kan bacin azumin jahilin da ya gaza sani banda jahilin da ke kokwanton shin wannan kan iya karya azumi na ko a'a amman a nan banda ci da sha da jima'i na daga abubuwan da ke karya azumi, shi jahili gaganci ne kawai ba a son ya shiga cikin karya azumin sa a hujjar sharia.
*(M: 1014): Idan aka tilasta mai azumi kan ci, sha ko jima'i ya bata azumin sa da dayan su azumin sa ya baci, haka nan idan bisa takiyya ya karya daidai ne cewa ya karya azumi bisa takiyya – kamar ya karya azumi ranar idin su bisa takiyya – ko ya zama lokacin azumi ne kamar cin abinci kan (lokacin) magriba, ya wajaba ya karya azumin a lokacin amman ya rama azumin daga baya, amman idan aka tilasta shi ya karya ba ta dayan hanyoyi ukun da mu ka kawo ba ko ya yi (azumin) bisa takiyya a nan akwai ishkali dangane da ramuwar sa, amman ba zai fita daga yankan shakku ba kan cika zumin kuma ya rama shi.
*(M: 1015): Da kishirwa za ta galabaitar da mai azumi ya ji tsoron jure mata sabida zai iya cutuwa ko kuma ya na da larurar da ba zai iya jure ta ba ya haltta ya sha daidai bukatar sa amman kada ya kara kan haka don yanke shakka, don shan fiye da kima kan iya karya azumi, wajibi ne ya kame bakin sa don ladabtar da kan sa a ragowar ranar amman idan a ramadana ne bisa yanke shakka (ihtiyadi), amman idan a wanin ramadana ne na wajibin yalwa ko wand aka ayyana ba dole sai ya kama bakin sa ba.