متن احکام
(M: 1013): Karahiya ne ga mai azumi ya yi shafi mace, sumbata, ko ya yi wasa da ita kamar yadda magabatan malamai (RA) su ka fada ko da ya na da tabbacin ba zai kawo ba, idan ya yi nufin ya kawo ya na da hukuncin wanda ya yi niyyar karya azumi, karahiya ne ya yi amfani ko alaka da abin da kanshin sa ko dandanin sa zai iya kai cikin makogaro ba kamar Turaren wuta da turare, haka nan shiga lambu don gudun gajiya, fitar da jinin da kan iya sa raunin jiki, shakar da ta shiga makogaro bisa kuskure, shinshina fure mai tsananin kanshi, jika kayan da ke jiki da ruwa, zaman mace cikin ruwa, dogara da wani abu mai tauri da zai amfanar don saukaka azumi, cire hakori ko wani abu da kan iya sa cikin baki jini, asuwaki da danyen itace, wasa da yin kuskurar baki, raira waka sai dai cikin wuraren Ayimmatu Ahlulbait (AS) da yabon su. Ya zo cikin labari cewa: (idan ku na azumi ku kiyaye harsunan ku daga karya, ku kame gannen ku kada ku yi jayayya da hassada da barna da dagawa da karya da yi wa juna mummunan kallo da ku saba da fushi da zagi juna da kunyata juna da jefi juna da munanan kalmomi da jayayya da gayawa juna munanan kalamai da zaluntar juna da wauta da soki juna haka nan ma kada ku gafala daga ambaton Allah (s.a.w)) hadisin na da tsayi.
*KARIN BAYANI:
*(M: 1008): Shakuwa ta halatta ga mai azumi ko da akwai yiyuwar fitowar wani abu daga cikin sa (ta baki), don yakke shakka an so idan da hali kada mutum ya yi matukar ya sa wani abu kan iya fitowa wanda za a iya ganin sa kamar amai, idan ba haka ba bai halatta ba.
*(M: 1009): Da wani abu zai fito daga sabida gyatsa sai ya koma ba tare da niyyar mayar da shi ba azumin sa na nan, amman da zai shigo cikin baki sannan a mayar da shi da gangan azumin sa ya baci sai ya rama a bisa yankan shakku kuma dole sai ya rama azumin kuma ya hada da kaffara.
*(M: 1010): Idan mutum ya hadiyi wani abu bisa mantuwa amman sai ya tuna kafin shigar sa makogaro wajibi ne ya fito da shi kuma azumin sa na nan, amman da a ce bai tuna ba sai da abin ya kai zuwa inda ba damar ya dawo da shi zuwa cikin bakin sa ba dole sai ya fito da shi ko ya amayo shi ba, idan kuma ya na kokwanto cikin abin da ya gabata dole ya fito da shi.
*(M: 1011): Idan mai azumi ya hadiyi abin da zai yi amansa ko ya sa shi da rana azumin sa ya baci idan ya yi aman da rana, ko da bai niyyaci kin aman ba – matukar ya san zai tashi da azumi – a lokacin da ya san bai kamata ya jinkirta niyya ba bisa gangancin da zai hana ya mike da niyyar sa kamar yadda ya zo cikin (M: 976), ba banbanci takanin sa da wanda ya yi niyyar amai da rana ko da bai yi aman ba.
*(M: 1012): Sanya zobe ba ya karya azumi, ko dafawa yara abinci, ko dandanon da mace ke yi wa abinci da makamantan su matukar ba za su kai ga makogaro ba, ko yin amai tare da niyya ba, manta ya na azumi – da a ce ya na sane ya yi aman azumin sa ya baci ko kadan nen – haka nan ba laifi da dandana ko lasar wani abu ko da an ji dandanon sa a cikin bakin sa – matukar bai wuce ciki ba – ko dayan m'aurata ya tsotsi harshen daya, ihtiyadin da aka fi so a nan kada ya zama akwai danshi a harshen wanda aka tsotsa, sadai an so yin aiki da ihtiyadi wajan.