متن احکام
An yi rangwamen shan azumin ramadana ga mutane kamar haka:
(Daga cikin su) akwai tsoho da mai kishirwar da azumi ya gagare shi, haka nan ga wanda ya ke da wani ciwo ko wahala a kan sa sai dai ciyar da mudun abinci duk ranar azumi ta kama shi, mafifcin abin da za a ciyar an fi son sa daga al'kama, musamman ma mudun ta biyu, an fi son hakan ma bisa ihtiyadi, ramuwa bata wajaba a kan sa daga baya ba ko da ya samu damar ramuwar duk da cewa an so bisa ihtiyadi da ya rama idan ya samu dama daga baya.
*(Daga cikin su) akwai mai tsohon cikin da azumin kan iya cutar da ita ko abin da ke cikin ta, da mai shayarwar da ke da karancin nono matukar azumin zai cutar da ita ko abin da ta ke shayarwar, amman ita za ta rama azumin daga baya, haka nan akwai ciyarwa a kan ta, ba tare da lissafin cewa mudun kan kosar ba ko a'a wajan ciyarwar ba tare da bambanci ba daga wuraren marawaita.
*(M: 1042): Babu bambanci ga mai shayarwar da dan ta ne ko ba na ta ba, idan ba na ta bane, ihtiyadin wajabci an so ta yi kokarin idan akwai hanyar da za ta iya bi wajan shayar da yaron ko da kuwa da wani abinci ne daban ba nonon ta ba kamar madara, idan hakan ta gagara ta iya shan azumin ta.
*Sharudan Ingancin Azumi da na Wajabcinsa
*(M: 1026): An shardanta ingancin azumi da abubuwa masu zuwa
1- Musulunci, azumi ba ya inganta ga kafiri, na'an idan da zai musulunta a yammacin ramadana amman bai yi wani abu da zai iya karya azumi ba a ranar kafin shigar sa musuluncin a bisa yankan shakku a na bukatar ya kame a lokacin da ya rage da niyya amman ya rama idan bai kame baki a ranar ba, amman ba a lura da imani wajan ingancin sa – a na nufin sauke nauyi – duk da cewa ya kan sanya fifikon lada.
2- Hankali da cikar haiyyaci (rashin buguwa da sauran su), da zai wayi gari ya na mai azumi sai ya haukace ko ya shiga yanayin da bai san halin da ya ke ciki ba har ranar ta fita azumin ranar bai yi ba, na'am idan ya kwanta da niyyar sauke farali kamar yadda mu ka ce ya dauka kawai ya na da azumi sai kuma ya rama bisa ihtiyadi.
3- Tsarki daga haila ko biki, azumi ba ya inganta ga mai haila ko nifasi ko da kuwa cikin wani yanki ne na wunin.
4- Yin asuba ba tare da janaba ba, ko faruwar hadasin janaba, haila ko nifasi kamar yadda mu ka yi bayani a baya.
5- Loacin zaman gida ba cikin halin tafiya ba kuma tafiyar da ta kai haddin kasaru, cikin wannan hali har azumin wajibi ma bai wajaba ba, banda a wurare uku:
Na daya: Kwanaki ukun kwana goman da mutum ya kasa yanka a hajjin tamattu'i.
Na biyu: Azumin kwana goma sha takwas, wadanda aka yi su maimakon kaffara ta wanda ya bar arfa kafin magriba.
Na uku: Azumin nafila na kayyadajjen lokaci, wanda a kayi bakancen yin sa a tafiya ko na sama da shi har ma a zaman gida. Haka nan bai halatta a yi azumin nafila tafiya ba, in banda kwanaki ukun hajji a Madina mai haske, ihtiyadi kwana ukun su zamo cikin laraba, al'hamis da juma'a.
*(M: 1027): Azumin jahilin matafiyi ya yi – jahilcin na sa na rashin sanin asalin hukuncin ne ko na abin da ya kebancin azumin ko na maudu'i ne, idan kuma ya sa, idan kuma ya san hukuncin amman ya aikata azumin sa ya baci, azumin mai tafiyar da ya yi bisa mantuwa ba yi ba amman bisa ihtiyadi (yankan shakku).
*(M: 1028): Azumin mai tafiyar da cika azumi ya kama shi ko da tafiyar sa bisa sabo ne da makamancin sa, amman ba azumi ga wanda ke da zabi kan cika azumi ko kasaru wato matafiyin da ke kan hanyar zuwa wurare hudu: Makka, Madina mai haske, Kufar Imam Ali, Haramin Imam Hussain (AS).
*(M: 1029): Ba azumi ga mara lafiya – daga cikin su akwai mai dundumi – idan azumin zai cutar da shi kamar ta tsanantar ciwon, jinkirin warkewa ko karin zafin ciwo, gwargwadon yadda zai kai a ce an cutu, ba bambanci kan haka tsakanin yakini, zato ko tsammani mai karfi wajan yiyuwar cutuwa idan an yi azumin, haka nan ba azumi ga mara lafiyar da ke tsoron kamuwa da cuta idan ya yi ballantana ma a ce ya san tabbas zai kamu da ita idan ya yi azumin, akwai azumi ga mara lafiyan da azumi ba zai cutar da shi da komai ba ya kuma wajaba a kan sa.
*(M: 1030): Ba dama a karya azumi kan dalilin gajiya ko da kuwa gajiyar ta wuce gona da iri sai dai in gajiyar ta kai yadda ba yadda zai iya azumi sai ya bar azumin amman ya rama daga baya, haka nan idan gajiyar za ta sa ya kai yadda ko abubuwan rayuwa ma ba zai iya ba har ma makamancin sa, ko kuma ma'aikacin da ke cikin tsananin kishirwar da ba zai iya kai azumin ba, amman domin yanke shakku a na bukatar takaituwa da ci ko sha gwargwadon bukatuwa ba a son ci ko sha barkatai.
*(M: 1031): Idan mutum ya dauki azumi ba tare da tuananin zai iya cutuwa ba sai daga baya hakan ta bayyanar masa cewar zai cutu akwai matsala kan ingancin azumin sa ko da cutarwar ta kai yadda ba za ta bar shi ya yi ba to kada ya dauka ya na azumi don cika ihtiyadi, da kuma ya yi azumi cikin tsoron ko firgicin cutuwa bashi da azumi, idan kuma ya gwada jure yanayin don neman kusanci ga Allah sai yanayin ya dore lafiya har zuwa karshen azumin sa a nan azumin sa ya yi.
*(M: 1032): Umarnin likita idan ya jawo zaton cutuwa ko tsananin tsoro kan yiyuwar cutuwa ba laifi ya ajiye azumi, haka nan ma ajiye azumin na wajaba da umarnin sa, sa likita zai ce: za ka iya azumi, amman mara lafiyar na tsoron cutuwa ba komai idan bai yi ba, amman idan tsoron ya doru kan tsananin zato ne rashin azumi kan iya haramta, idan ba haka ba azumi ya halatta a kan sa kuma ya kan isu da zai yi ba tare da cutuwa ba yayin ko bayan azumin.
*(M: 1033): Idan mara ya warke kafin zawali bai yi wani abu da kan iya karya azumi ba, domin yanke shakku a na son ya niyyaci azumi kuma ya rama daga baya.
*(M: 1034): Azumin yaron ya ke iya bambance ayyukan ibada ya inganta.
*(M: 1035): Ba azumin nafila ga wanda ke da bashin ramadana a kan sa, na'am amman idan ya manta ramuwar da ke kan sa sai ya tuna bayan kammala na nafilar azumin sa ya yi.
Wanda ke da azumin kaffara a kan sa zai iya yin na nafilar ko ramuwar bakance ko na haya da makamntan sa.
*(M: 1036): Wajabcin azumi na bukatar: balaga, hankali, zaman gida, haiyyaci (rashin maye), koshin lafiya da tsarkaka daga haila ko biki.
*(M: 1037): Da yaro zai yi azumin nafila sai ya balaga cikin ranar ba wajabcin cika azumin duk da cewa a na matukar son ya cika don yanke shakku, da a ce zai samu kan sa cikin hauka ko buguwa cikin lokacin bayan niyyatar azumin sa ihtiyadi shi ne ya cika azumin sa idan kuma bai cika ba sai ya rama daga baya.
*(M: 1038): Idan ya yi tafiya kafin zawali dole ya sha azumi musamman ma idan tun dare ya yi nufin tafiyar, idan kuma bayan zawali ya yi tafiyar sai ya cika azumin sa bisa ihtiyadi (yanke shakka) musamman idan bai yi niyyar tafiyar ba cikin daren ranar, idan kuma bai karya azumin sa har ya dawo karin sa ko garin da zai zo, a nan idan ya shiga garin kafin zawali sai ya cika azumin sa domin yanke shakka kuma ya isu da hakan, idan kuma bayan zawali ya je ba shi da azumi, da zai yi azumi bai zai isu gare shi ba bisa ihtiyadi, idan ya yi abin da kan iya kartya azumin sa cikin tafiyar ya shiga garin kafin magriba a na bukatar ya kama bakin sa zuwa magribar.
*(M: 1039): Abun lura game da tafiya shine kafin zawali da bayan sa – haka nan yayin dawo masa – shi ne garin da bai kai haddin kasaru ba, na'am ba ya halatta ga matafiyi ya karya azumi har sai ya kai nisan da zai haddin kasaru da zai karya azumi da gangna tare da sanin hukuncin karyawar dole ya yi kaffara.
*(M: 1040): Ya halatta yin tafiya cikin ramdana ko da don bukatar shan azumi ne sai dai makaruhi ne, sai dai cikin aikin hajji ko umra, ko yaki sabida Allah, ko tsoron salwantar wata dukiya, ko tsoron halakar wani mutum.
Tafiya bata kamaci wanda ke da azumin haya a kan sa da makamantan su, haka nan rana ta uku cikin kwanakin i'itikafi, amman ya halatta idan ya azumin bakance ne, game da na rantsuwa ko wanda aka yi alkawarin sa akwai ishkali amman sai ya yi azumin sa bisa ihtiyadi.
*(M: 1041): Ya halatta cika ciki da ci ko sha ga matafiyi haka nan ma jima'i da rana amman bisa karhancin su an so bisa yankan shakku a bar su baki daya musamman ma jima'i.