متن احکام
Azumi na daga cikin mustahabbai karfafa, an rawaito cewa garkuwa ne daga wuta, zakkar jiki ne, bawa na iya shga al'janna sabida shi, baccin mai azumi ibada ne, nunfashin sa da shirun sa tasbihi ne, aikin sa karbabbe ne, addua'r karbabbiya ce, warin bakin sa wajan Allah (s.a.w) ya fi kamshin turare, mala'iku na yi masa addu'a har ya gama, ya na da farin ciki kala biyu farin ciki yayin buda bakin sa da farin ciki yayin haduwa da ubangijin sa.
*(M: 1064): Daidaikun azumin nafila na da yawa, an karfafa son yin azumin kwana uku cikin kowane wata, mafi falalar sa an fo son ya zama cikin alhamis din farkon kowane wata, da ta karshen sa, da larabar farkon goman tsakkiya, azumin ranar ghadir domin ya yi daidai da – kamar yadda ya zo cikin ruwayoyi – hajji da umra dari zababbu karbabbu, da azumin ranar da aka haifi Manzon Rahama (SAW) da ranar aiko shi (SAW), da ranar (da aka) shimfida kasa – ita ce ranar ishirin da biyar ga zulkida – da ranar arfa ga wanda azumin ba zai gajiyar da shi wajan ibada ba amman da sharadin rashin kokwanton kan wata, Ranar mubahala itace ranar ishirin da hudu na zulhijja, watan rajab, watan sha'aban, da wasu ranakun da su ke da falala bisa ydda wasu ke gani hakana fifikon wasu kan wasu shi ma kamar yadda wasu ke gani, ranar da ake kira da ranar nuuruz (ranar farko ta shekarar shamsiyya wadda ta yi daidai da 21 na kowane March, ranar farko ta biyu da ta bakwai cikin watan muharram, uk ranar alhamis da juma'a, matukar ba ta a ranar idi ba.
*(M: 1065): An karhanta azumi cikin: Azumi ranar arfa ga wanda ya san zai iya gajiyar da shi wajan yin addu'a, da ranar da a ke tsananin kokwanton kan shin idin karamar salla ne ko karshen ramadana, azumin bako na nafila ko na wajibin da ba a aiyyana lokacin yin sa ba idan ba izinin wanda ya sauke shi, da azumin yaro na nafila in ba izinin uban sa.
*(M: 1066): Ya haramta azumi ranar idi, da ranar tashrik wato ranar 13, 14 da 15 da zulhajji ga wanda ya ke a Minna da niyyar hajji ya ke zaune ko kuwa, da ranar da ake kokwanton cewa shin cikin ramadana ne ko shauwal, da bakancen haram shine kamar ya yi bakancen aikata haramun domin godiya, ba laifi ga azumin tsawa, azumin dore shi ne azumin dare da yini har zuwa farkon wani daren, azumin kwana biyu ba tare da an sha ko ci wani abu a tsakani ba, ba laifi ga jinkirta buda baki har zuwa dare na biyu idan bai da niyyar wani azumin a washe gari, ihtiyadin mustahabbi ba a son kai azumi zuwa dare na biyu an so a ci ko a sha wani abu.
*(M: 1067): Ihtiyadin mustahabbi an so mace kada ta yi azumin nafila ko na wajibin da ba ta aiyyana lokacin sa ba sai da izinin mijin ta duk da cewa ya halatta in har ba zai shiga hakkin mijin na ta ba, kada ta tsallake ihtiyadi matukar ya hana ta idan ba zai takura hakkin sa ba.