| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 7 | 1 | 1 | 1 | مكه |
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai. ١ Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu; ٢ Mai rahama, Mai jin ƙai; ٣ Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako. ٤ Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa. ٥ Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya. ٦ Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba. ٧