«العاديات»

لیست سوره‌ها

اطلاعات سوره

تعداد آیه حزب جزء صفحه‌ی شروع محل سوره
11 120 30 599 مكه

متن سوره

Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. ١ Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. ٢ Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. ٣ Sai su motsar da ƙũra game da shi. ٤ Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. ٥ Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. ٦ Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka. ٧ Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. ٨ Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. ٩ Aka bayyana abin da ke cikin zukata. ١٠ Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? ١١