| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 11 | 120 | 30 | 600 | مكه |
Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)! ١ Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? ٢ Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? ٣ Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. ٤ Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. ٥ To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. ٦ To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. ٧ Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). ٨ To, uwarsa Hãwiya ce. ٩ Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? ١٠ Wata wuta ce mai zafi. ١١