| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 8 | 120 | 30 | 600 | مكه |
Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku). ١ Har kuka ziyarci kaburbura. ٢ A'aha! (Nan gaba) zã ku sani. ٣ Sa'an nan, tabbas, zã ku sani. ٤ Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni. ٥ Lalle ne da kuna ganin Jahĩm. ٦ Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane. ٧ Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku). ٨