«الهمزة»

لیست سوره‌ها

اطلاعات سوره

تعداد آیه حزب جزء صفحه‌ی شروع محل سوره
9 120 30 601 مكه

متن سوره

Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa). ١ Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa. ٢ Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi. ٣ A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama. ٤ Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama? ٥ Wutar Allah ce wadda ake hurawa. ٦ Wadda take lẽƙãwa a kan zukata. ٧ Lalle ne ita abar kullẽwa cea kansu. ٨ A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu. ٩