| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 7 | 120 | 30 | 602 | مكه |
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako? ١ To, wannan shi ne ke tunkue marãya (daga haƙƙinsa). ٢ Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci. ٣ To, bone yã tabbata ga masallata. ٤ Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu. ٥ Waɗanda suke yin riya (ga ayyukansu) ٦ Kuma suna hana taimako. ٧