| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 3 | 120 | 30 | 603 | مدینه |
Idan taimakon Allah ya zo da cin nasara. ١ Kuma ka ga mutane suna shiga addinin Allah, ƙungiya-ƙungiya. ٢ To, ka yi tasbihi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka nẽme Shi gafara, lalle Shi (Ubangijinka) Ya kasance Mai karɓar tũba ne. ٣