| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 5 | 120 | 30 | 603 | مكه |
Hannãye biyu na Abũlahabi sun halaka, kuma ya halaka. ١ Dũkiyarsa ba ta tsare masa kõme ba, da abin da ya tãra. ٢ Zã ya shiga wuta mai hũruwa. ٣ Tãre da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta). ٤ A cikin kyakkyãwan wuyanta akwai igiya ta kaba (Rãnar ¡iyãma). ٥