| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 6 | 120 | 30 | 604 | مكه |
Ka ce "Ina nẽman tsari ga Ubangijin mutãne." ١ "Mamallakin mutane." ٢ "Abin bautãwar mutãne." ٣ "Daga sharrin mai sanya wasuwãsi, mai ɓoyewa." ٤ "Wanda ke sanya wasuwãsi a cikin ƙirãzan mutane." ٥ "Daga aljannu da mutane." ٦