«الصافات»

لیست سوره‌ها

اطلاعات سوره

تعداد آیه حزب جزء صفحه‌ی شروع محل سوره
182 89 23 446 مكه

متن سوره

Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). ١ Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. ٢ Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. ٣ Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. ٤ Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. ٥ Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. ٦ Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. ٧ Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. ٨ Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. ٩ Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. ١٠ Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. ١١ Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. ١٢ Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. ١٣ Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. ١٤ Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." ١٥ "Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? ١٦ "Ashe kõ da ubanninmu na farko?" ١٧ Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." ١٨ Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. ١٩ Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." ٢٠ Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. ٢١ Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. ٢٢ Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. ٢٣ Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. ٢٤ Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? ٢٥ Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. ٢٦ Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. ٢٧ Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." ٢٨ Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. ٢٩ "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." ٣٠ "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." ٣١ "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." ٣٢ To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. ٣٣ Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. ٣٤ Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. ٣٥ Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? ٣٦ Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. ٣٧ Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. ٣٨ Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. ٣٩ Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. ٤٠ Waɗannan sunã da abinci sananne. ٤١ 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. ٤٢ A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. ٤٣ A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. ٤٤ Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. ٤٥ Farã mai dãɗi ga mashãyan. ٤٦ A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, ٤٧ Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. ٤٨ Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. ٤٩ Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. ٥٠ Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." ٥١ Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" ٥٢ "Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" ٥٣ (Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" ٥٤ Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. ٥٥ Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." ٥٦ "Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." ٥٧ "Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." ٥٨ "Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" ٥٩ Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. ٦٠ Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. ٦١ Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? ٦٢ Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. ٦٣ Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. ٦٤ Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. ٦٥ To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. ٦٦ Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. ٦٧ Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. ٦٨ Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. ٦٩ Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. ٧٠ Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. ٧١ Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. ٧٢ Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. ٧٣ Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. ٧٤ Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. ٧٥ Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. ٧٦ Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. ٧٧ Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. ٧٨ Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. ٧٩ Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ٨٠ Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. ٨١ Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. ٨٢ Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. ٨٣ A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. ٨٤ A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" ٨٥ "Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" ٨٦ "To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" ٨٧ Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. ٨٨ Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." ٨٩ Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. ٩٠ Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? ٩١ "Me ya sãme ku, bã ku magana?" ٩٢ Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. ٩٣ Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. ٩٤ Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, ٩٥ "Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" ٩٦ Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." ٩٧ Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. ٩٨ Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." ٩٩ "Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." ١٠٠ Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. ١٠١ To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." ١٠٢ To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. ١٠٣ Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" ١٠٤ "Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ١٠٥ Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. ١٠٦ Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. ١٠٧ Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. ١٠٨ Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. ١٠٩ Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ١١٠ Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. ١١١ Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. ١١٢ Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). ١١٣ Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. ١١٤ Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. ١١٥ Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. ١١٦ Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. ١١٧ Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. ١١٨ Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. ١١٩ Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. ١٢٠ Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ١٢١ Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. ١٢٢ Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. ١٢٣ A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" ١٢٤ "Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" ١٢٥ "Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" ١٢٦ Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). ١٢٧ Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. ١٢٨ Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. ١٢٩ Aminci ya tabbata ga Ilyãs. ١٣٠ Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. ١٣١ Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. ١٣٢ Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. ١٣٣ A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. ١٣٤ Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). ١٣٥ Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. ١٣٦ Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. ١٣٧ Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? ١٣٨ Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. ١٣٩ A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. ١٤٠ Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. ١٤١ Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. ١٤٢ To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, ١٤٣ Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. ١٤٤ Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. ١٤٥ Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. ١٤٦ Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). ١٤٧ Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. ١٤٨ Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" ١٤٩ Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? ١٥٠ To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. ١٥١ "Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. ١٥٢ Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? ١٥٣ Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? ١٥٤ Shin, bã ku tunãni? ١٥٥ Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? ١٥٦ To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. ١٥٧ Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" ١٥٨ Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. ١٥٩ Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. ١٦٠ To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, ١٦١ Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. ١٦٢ Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. ١٦٣ "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." ١٦٤ "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." ١٦٥ "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." ١٦٦ Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, ١٦٧ "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." ١٦٨ "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." ١٦٩ Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. ١٧٠ Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. ١٧١ Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. ١٧٢ Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. ١٧٣ Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. ١٧٤ Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. ١٧٥ Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? ١٧٦ To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. ١٧٧ Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. ١٧٨ Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. ١٧٩ Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. ١٨٠ Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. ١٨١ Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. ١٨٢