| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 11 | 119 | 30 | 596 | مكه |
Inã rantsuwa da hantsi. ١ Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa). ٢ Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba. ٣ Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko. ٤ Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda. ٥ Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma? ٦ Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai? ٧ Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka? ٨ Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi. ٩ Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa. ١٠ Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya). ١١