| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 8 | 119 | 30 | 596 | مكه |
Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)? ١ Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe. ٢ Wanda ya nauyayi bãyanka? ٣ Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka? ٤ To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. ٥ Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. ٦ Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah). ٧ Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi. ٨