| تعداد آیه | حزب | جزء | صفحهی شروع | محل سوره |
|---|---|---|---|---|
| 8 | 120 | 30 | 597 | مكه |
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn. ١ Da Dũr Sĩnĩna. ٢ Da wannan gari amintacce. ٣ Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. ٤ Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni ٥ Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. ٦ To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)? ٧ Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba? ٨