«القدر»

لیست سوره‌ها

اطلاعات سوره

تعداد آیه حزب جزء صفحه‌ی شروع محل سوره
5 120 30 598 مكه

متن سوره

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi (Alƙur'ãni) a cikin Lailatul ƙadari (daren daraja) ١ To, me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul ¡adari? ٢ Lailatul ¡adari mafi alheri ne daga wasu watanni dubu. ٣ Mala'iku da Rũhi suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabõda kowane umurni. ٤ Sallama ne shi daren, har fitar alfijiri. ٥